A cewar kafar yada Labarai ta Hauza, a cikin rayuwar yau da kullum, mu’amaloli na kuɗi da hulɗar tattalin arziki suna daga muhimman sassan zamantakewarmu. A cikin wannan tsari, batun bashi da biyan hakkokin mutane ba kawai wajibin kuɗi ba ne, har ma nauyi ne na ɗabi’a da kuma na shari’a da aka jaddada -maida hankali akansa a koyaushe.
Wani lokaci yana iya faruwa cewa saboda wasu dalilai mutum ba shi da ikon biyan adadin bashin gaba ɗaya a lokacin da ya yi - alkawari, amma sai tambaya ta taso: idan mutum yana da ikon biyan wani ɓangare na bashin, shin yana da hurumin ya jinkirta biyan ko ƙayyade wani lokaci dabam?
Mai girma Ayatullahi al-Uzma Khamenei sun ba da amsa kan wannan tambaya, wacce ake gabatar da ita ga masu sha’awa.
Tambaya: Idan muna da bashi ga wani, kuma muna da ikon biyan wani ɓangare na bashin, amma ba mu biya ba ko muka jinkirta zuwa wani lokaci, shin hakan zunubi ne a shari’a?
Amsa: Da zarar lokacin biyan bashi ya yi kuma mai bada bashi ya nemi hakkinsa, wajibi ne a kan mai - biyan bashi ya biya gwargwadon iyawarsa. Yin jinkiri wajen biyan abin da zai iya biya kuwa zunubi ne.
Your Comment